Amirka ta mika wasu fursunan guantanamo
November 16, 2015Kasar Amirka ta bada sanarwar mika wasu firsunan guantanamo su biyar zuwa ga Hadaddiyar Daular Larabawa a jiya Lahadi a wani mataki na soma shirye-shiryen rufe gidan kason wanda ke da akwai babbar mahawara a kansa.
Ma'aikatar tsaron Amirka ta Pantagon ta ce kawo yanzu Firsunoni 107 ne dai ke ci gaba da kasancewa a cikin wannan gidan kaso na Guantanamo. Kuma ta bayana godiya ga gwamnatin Hadaddaiyar Daular Larabawar kan abin da ta kira kokarin na taimakon Amirka a cikin shirin na rufe wannan gidan kaso.
A shekar ta 2002 ne dai kasar ta Amirka ta bude wannan gidan kaso domin tsare 'yan ta'adda da suka hada da wadanda ake zargi da hannu a cikin kitsa harin ranar 11 ga watan Satumba. Rufe wannan gidan kaso na guantanamo dai na daga cikin alkawurran da Shugaba Obama ya dauka kafin cikar wa'adin milkinsa a watan Janairun shekara ta 2017.