Amirka ta lalata wata tungar ISIS a Iraki | Labarai | DW | 09.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta lalata wata tungar ISIS a Iraki

Rundunar sojin saman Amirka ta kai wa 'yan kungiyar ISIS farmaki a birnin Irlib sakamakon addabar Kiristocin yankin da suka yi.

Amirka ta bayyana cewar jiragenta na yaki sun kai hare-hare a kan mayakan masu kaifin kishin addini a birnin Irlib na Iraki, da zummar ja musu birki a yunkurin da suke yi na mamaye kasar tare da kafa shari'ar musulunci. Ba a dai bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata a wadannan hare-hare ba. Hakazalika fadar White House ba ta fayyace lokacin da za ta diba na kai musu farmaki ba.

Dubban Kiristoci da kuma 'yan tsiraru ne suka tsere daga gidajensu tun bayan da 'yan Kungiyar IS wato ISIS suka karbe ikon garuruwansu na asali ciki kuwa har da Mosul. Yanzu haka ma dai masu kaifin kishin addinin na ci gaba da kakkange madatsar ruwan da ta fi kowacce girma a Iraki, lamarin da wakiliyarmu ta ce yana barazana ga zamar lafiya a Iraki baki daya.

"Wannan tamkar wani makamin kare dangi ne, domin idan suka yanke shawarar lalata dam din, to ruwan zai shanye Mosul da kuma Bagadaza shi kansa. Idan suka barshi a yadda yake, wannan ma ya na nufin cewar su ne ke da iko kan madatsar ruwan. Ma'ana su ne za su bai wa mutane dubu 500 ruwa lokacin da suka ga dama."

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal