Amirka ta kai makamai Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 26.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta kai makamai Koriya ta Kudu

Ayarin farko na kayan yakin da Amirka ta tura zuwa Koriya ta Kudu da nufin taka birki ga shirin Koriya ta Arewa na makaman nukilya ya isa kasar.

Wannan na zuwa ne a dai-dai loakcin da Koriya ta Arewa ta gudanar da bikin nuna murna ga abin da ta kira nasarar da ta yi wajen atisaye mafi girma na makamin atilare. Shugaba Kim Jong-un da kansa ne dai ya jagoranci atisayen makaman da aka yi a garin Wonson na Gabashin kasar a dai-dai loakcin da kasar ke shirin gudanar da bikin zagayowar shekaru 85 da kafa rundunar sojin Koriya ta Arewa. Ana fargabar dai Koriya ta Arewar za ta yi amfani da lokacin bikin zagayowar ranar kafa rundunar sojin nata,wajen sake yin gwajin makamin nukiliya. Wannan atisayen gwajin makaman atilaren da Koriya ta Arewa ta yi na zuwa ne a dai-dai lokacin da tsamin dangantakar da ke da akwai tsakaninta da Koriya ta Kudu da kawarta Amirka ke kara kamari, inda har ma Amirkan ta fara jibge makaman yakinta a Koriya ta Kudun a wani abu mai kama da shirin kota kwana.