Rundunar Flintlock ta soma atisaye a Ghana
March 10, 2023Amirka ta kaddamar da wata rundunar soji da za ta taimaka wajen shawo kan barazanar tsaron da kasashen yammacin Afirka da dama ke fuskanta daga mayaka masu ikirarin jihadi, rundunar da ta kunshi sojoji daga kasashe akalla ashirin da tara, ta soma gudanar da atisaye a kasar Ghana, in da aka tsara yadda za a horas da sojojin na Afirka da dabarun yaki a yayin atisayen rundunar da aka yi wa lakabi da Flintlock.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu da ake zargin mayakan jihadi ne suka kai hari tare da hallaka wasu sojoji Burkina Faso kimanin goma sha daya a yayin da suka yi yunkurin kwace iko da wasu garuruwa a yankunan gabashi da arewacin kasar a daren ranar Alhamis da ta gabata. Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fama da ayyukan masu gwagwarmaya da makaman.