Amirka ta harbi jirgin kasar Iran | Labarai | DW | 19.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta harbi jirgin kasar Iran

Shugaba Donald Trump na kasar Amirka ya sanar da cewa jirgin ruwan yakin kasarsa ya yi nasarar harbe wani jirgin maras matuki mallakar kasar Iran a zirin Hormuz.

Shugaba Trump ya bayyana harbe jirgin ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar mulki ta White House a jiya Alhamis. Sannan ya jinjina wa namijin kokarin da matuka jirgin ruwan Amirkan suka yi na daukar matakin da ya dace cikin kankanin lokaci, bayan da suka tabbatar da cewar  jirgin na Iran na barazana ga rayukansu da kuma jirgin.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif wanda ke ganawa da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Guterres ya bayyana cewa bashi da masaniya game da faruwar wannan al'amari, kafin daga bisani ya ce Amirka ta harbe jirgin kasarta ne bisa kuskure 

Kafin faruwar wannan lamari dai an jiyo shugaba Trump na jan hankalin sauran kasashe da suyi Allah wadai da yadda Iran ta dauki aniyar ruguza 'yancin sufurin ruwa da kuma kasuwancin tsakanin kasashen duniya.