1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan bama-bamai kan mayakan jihadi a Siriya

Abdoulaye Mamane Amadou
August 31, 2019

Akalla mayakan jijhadi 40 ne suka hallaka a yayin da wani harin roka ya rutsa su lokacin da suke kaddamar da wani taro kusa da birnin Idleb na kasar Siriya.  

https://p.dw.com/p/3OoRN
Syrien Tote nach Luftschlägen bei Idlib
Hoto: picture-alliance/AA/I. Idilbi

Rahotanni daga yankin sun ce harin da ya rutsa da shugabannin kungiyoyin jihadi kamar su Hourra al-Din da Ansar al-Tawhid wadanda ke rike da akasarin yankin na Idleb an kai shi ne a yayin da suke gudanar da wani taron a cikin gona.

Wannan dai shi ne farmaki mafi muni da sojoji suka kai akan mayakan jihadin, kwanaki bayan wani makamancinsa da ya hallaka jiga-jigan kungiyoyin mayakan akalla takwas.

Tuni hukumomi a birnin Washington na Amirka suka bayayya matakin kai farmakin ga masu tayar da kayar baya.