Amirka ta hallaka mayaka 100 a Siriya | Labarai | DW | 08.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta hallaka mayaka 100 a Siriya

Sojoji da Amirka ke jagoranta a yaki da yan IS sun halaka mutane 100 a wani hari da suka kai kan mayaka masu goyon bayan shugaba Bashar al Assad a wani mataki na ramuwar gayya bayan da mayakan suka kai hari kan aminanta.

Rundunar hadin gwiwa da Amirka ke jagoranta wadda ke yaki da 'yan IS masu ikrarin jihadi ta ce ta kashe mayaka masu goyon bayan gwamnatin Siriya akalla su kimanin 100 a gabashin Siriya a daya daga cikin gumurzu mafi muni da aka gani.

Da farko sojoji masu goyon bayan shugaba Bashar al Assad ne suka kai hari kan wasu muhimman rijiyoyin mai a lardin Deir Ezzor da ke karkashin ikon sojin Kurdawa da Amirka ke marawa baya.

Wannan arangamar dai ta zo ne yayin da ake samun karuwar tsamin dangantaka tsakanin Washington da Dmascus game da batun amfani da makamai masu guba da ake zargin sojojin gwamnatin Siriya da mayakan sa kai masu goyon bayanta da aikatawa.

A halin da ake cikin kuma sojojin gwamnatin Siriyar sun ci gaba da ruwan bama bamai a rana ta hudu a jere a yankin dake hannun yan adawa a gabashin Ghouta dake wajen Damascus.