Amirka ta gargadi Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 23.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta gargadi Sudan ta Kudu

An kirayi shuwagabannin Sudan ta Kudu su kawo karshen fada a kasar ko su fuskanci takunkumi daga Majalisar Dinkin Duniya.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, ya kirayi shugabannin kasar Sudan ta Kudu da su warware takaddamar rikici da ya ki ya ki cinyewa a kasar ko su fuskanci fushin Majalisar Dinkin Duniya da ma sanyawa kasar takunkunmin sayan makamai.

Wannan mataki na jan kunne ga Sudan ta kudu na zuwa ne bayan fara ziyara da John Kerry ke yi a wasu kasashen Afirka da nufin inganta tsaro, inda ya gana da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyata da wasu ministocin harkokin wajen kasar Somaliya da ma dukkanin bangarori daga Sudan har da Sudan ta Kudu dan samo bakin zaren warware rikicin Sudan ta kudu ke fama da shi. Mr. Kerry ya kuma nemi hanyar sake tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.

Fadan ya sake barkewa a Juba babban birnin kasar a karshen watan Yulin da ya gabata, ya hadda shakku ga jaririyar kasar na sake fadawa yakin basasa.