SiyasaJamus
Amirka ta gabatar da kudurin raya kasa
April 1, 2021Talla
Shugaba Biden ya ce ware zunzurutun kudin zai bayar da damar gudanar da ayyukan da kasar ta sami koma baya a kansu tare da ma yin gogayya da China da ke zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.
Amirkar na sa ran shirin da zai kwashe tsawon shekaru takwas ya samar da miliyoyin guraben ayyuka. 'Yan jam'iya mai mulki ta Democrat dai sun yi maraba da kudurin tare da fatan jam'iyyar hamayya ta Republican ta mara musu baya.