1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Trump ta sami nasara kan dokar hana shiga kasa

Ramatu Garba Baba
June 26, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yaba da hukuncin kotun kolin kasar na amincewa da dokar hana wasu kasashen musulmi shiga kasar, shugaban ya ce wannan nasara ce ga al'ummar Amirka dama kasa baki daya.

https://p.dw.com/p/30LPo
USA Washington Supreme Court
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. S. Applewhite

Trump ya yaba da hukuncin kotun inda nan take ya yi shelar neman amincewar 'yan majalisar kasar don samun kudin da za a yi anfani a gina karin shingaye a kan iyakokin kasar.

Kotun ta yi watsi da bukatar da aka shigar gabanta kan cewa, dokar an tanade ta ne don nuna wariya ga al'ummar musulmi da ke sha'awar shiga kasar daga kasashen Iran da Siriya da Yemen da Somaliya da kuma Libya da wannan doka ta shafa. Mai shari'a Cif Justice John Roberts ya ce, kowanne shugaban kasa na da karfin iko kan dokokin shige da fice a kasa.

An kwashi tsawon watanni ana kai ruwa rana kan wannan batu bayan da Trump ya sanar da hana wasu kasashen duniya shiga kasar. Tun bayan shan rantsuwar soma aiki, shugaban  ya sha alwashin kare muradun 'yan kasa dama tabbatar da tsaro ga daukacin al'umma.