1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dawo da takunkuman MDD kan Iran

Abdoulaye Mamane Amadou
September 20, 2020

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya bayyana cewa takunkuman Majalisar Dinkin Duniya kan Iran za su soma aiki daga jiya Asabar, kana Washington zata ladabta duk wanda ya bijirewa matakin.

https://p.dw.com/p/3ikH9
Iran Atomanlage Fordo
Hoto: AFP/Atomic Energy Organization of Iran/HO

Har yanzu Amirka na kan bakarta ta sake kakaba takunkumai ga gwamnatin Iran game da batun aikinta na bunkasa makamashin nukiliya, duk da yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran a shekarar 2015, da ma turjiyar da take fuskanta daga sauran kawayenta musamman ma na nahiyar Turai.

Sai dai a nata bangare gwamnatin Iran ta bakin ministan harkokin wajenta Mohammad Javad Zarif, ta bayyana a ranar Asabar da cewar batun sake kakaba takunkuman wani shaci fadi ne kawai na gwamnatin Amirka.