Amirka: Najeriya ta daina tauye hakkin addini | Labarai | DW | 18.11.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Najeriya ta daina tauye hakkin addini

Amirka ta janye Najeriya daga jerin kasashen da ba sa bayar da 'yanci addini, lokacin da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai isa Najeriya a ziyarar da yake yi a wasu kasashen Afirka.

Matakin da aka sanar a ranar Laraba na cikin jawabin da Blinken, inda ya ayyana sunayen kasashen da ke hana mutane yin addini yadda ya kamata. Kasashen da Amirka ta zayyana sun hada da Myanmar da China da Koriya ta Arewa da Saudiyya da Rasha da sauran wasu kasashe.

A shekarar da ta gabata Amirka ta sanya Najeriya cikin jerin kuma kawo yanzu ba ta bayar da dalilin janye sunan Najeriyar daga cikin jerin ba.

Ana dai sa ran sakataren harkokin wajen Amirkan zai isa Abuja a wannan Alhamis inda zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari.