Amirka na bukatar sabuwar dubara a Iraƙi | Labarai | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka na bukatar sabuwar dubara a Iraƙi

Wani babban sineta na jam´iyar Republican a Amirka ya yi kira da a samu wata sabuwar dubara ga Iraqi. A cikin wani jawabi da ya yiwa zaman majalisar dattijai Sineta Richard Lugar ya ce karin dakarun da aka yi a birnin Bagadaza ba ya aiki kana kuma kudi da asarar rayukan da ake yi ya fi ribar da ake samu a wannan yaki. Dan jam´iyar na Republican kuma babban wakilin ta a kwamitin kula da harkokin ketare na majalisar dattijan ya yi kira ga shugaba GWB da ya rage yawan sojojin kasar a Iraqi kana kuma ya ba da muhimmanci ga bin hanyoyin diplomasiya da na tattalin arziki. Duk da haka dai Lugar ba yi kira da a janye dakarun Amirka gaba daya daga Iraqi ba. A jiya litinin sama da mutane 40 aka kashe a hare haren bama-bamai a fadin kasar ta Iraqi.