Amirka: Muna da karfin kare kanmu | Labarai | DW | 05.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Muna da karfin kare kanmu

Rundunar sojin Amirka ta ce ta na da karfin da za ta iya kare kanta daga dukkan wata barazana daga Koriya ta Arewa bayan da Koriya ta Arewan ta yi wani gwaji na makamin nukiliya mai cin dogon zango.

Jeff Davis da ke magana da yawun rundunar sojin ta Amirka ya bayyana cewa sun samu nasarar gwajin na'urar wargaza harin makami mai cin dogon zangon a watan da ya gabata wadda zai iya kare su daga dukkan wani harin da Koriya Ta Arewan ka iya kawo musu.

Wannan sanarwa da Amirkan ta fidda dai na zuwa ne daidai lokacin da danganta ke kara yin tsami tsakanin Washington da Pyongyang, batun da ya sanya wasu kasashe ciki kuwa har da Rasha da China yin kira da a gujewa yaki ko kawo sauyin gwamnati a duk yunkurin da za a yi wajen raba Koriya ta Arewa da makamanta masu linzami.