1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: kotu ta haramta wa bakin haure zama yan kasa

June 7, 2021

Dubun dubatar yan gudun hijira a kasar Amirka za su ci gaba da kasancewa masu neman mafaka a maimakon zama yan kasa na dundundun.

https://p.dw.com/p/3uYSk
TABLEAU | 100 Tage Biden
Hoto: Al Drago/Getty Images/AFP

Kotun kolin Amirka ta sake tabbatar da dokar nan ta haramta wa bakin haure masu neman mafaka da su ka shiga kasar ta barauniyar hanya, damar mallakar takardun zama yan kasar na dundundun.

Dokar na daya daga cikin dokokin da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya assasa, wadda kuma sabuwar gwamnatin shugaba Joe Biden ke kokarin sauyawa.

Hukuncin na kotun dai zai cigaba da shafar dubunnan yan gudun hijira da ke zaune a kasar ta Amirka domin nemar mafaka.