Amirka: Kalubalen zaben Najeriya | Labarai | DW | 11.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: Kalubalen zaben Najeriya

Kasar Amirka ta nunar da cewa babban zaben da za a gudanar a Tarayyar Najeriya cikin watan Fabarairu mai zuwa, na zaman wani zakaran gwajin dafi na dimukuradiyya a kasar.

Nigeria wählt Gouverneure und Regionalparlamente

Shirye-shiryen babban zabe a Najeriya

Mataimakin jakadan Amirka Jonathan Cohen ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya nunar da cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirkan tana da damuwa matuka kan yadda jami'an tsaron Najeriya ke cusgunawa mutane tare da shiga dumu-dumu cikin harkar siyasa. Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC mai mulki dai na neman wa'adi na byiu, yayin da yake fuskantar gagarumar adawa daga dan takarar babbar jam'iyar adawar ta PDP da kuma shugabar gwagwarmayar kwato 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace wato Bring Back Our Girls Oby Ezekwesili ta jam'iyyar ACPN.