1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Joe Biden ya nema hadin 'yan jam'iyyar Demokrat na Amirka

Abdoulaye Mamane Amadou
April 12, 2020

Tsohon mataimakin shugaban Amirka Joe Biden ya lashe zaben tantance gwani na tsayawa takara karkashin inuwar jam'iyyar Demokrat a jihar Alaska tare da bin matakan kariya daga annobar cutar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3aoGu
USA | Wahlen | Joe Biden und Bernie Sanders
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/E. Vucci

Dan takarar jam'iyyar Demokrat a Amirka Joe Biden ya lashe zaben fidda gwani na Jihar Alaska da aka gudanar a yammacin jiya da kuri'u kaso 53,3 cikin 100, inda ya bai wa abokin hamayyarsa Bernie Sanders rata wanda shi kuma ya tashi da kaso 44,7 cikin 100 kawai na adadin kuri'un da aka kada.

Rahotanni sun ce ko baya ga kuri'un da aka kada ta hanyar sakon gidan waya da intanet, tsohon mataimakin shugaban na Amirka Joe Biden, ya kuma samu karin wasu wakilai, inda tara daga cikin 15 na adadin masu hurumin na jefa kuri'a suka nuna masa goyon baya.

An tsara zaben kafin Sanders ya fice daga cikin takara a makon da ya wuce. Joe Biden ya yi kira ga magoya bayan Bernie Sanders kan ba shi goyon baya a zaben kasa baki daya inda zai fafata da Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican.