1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Haraji mafi girma kan kayan Turai

Abdullahi Tanko Bala
October 18, 2019

Barasa da cikwi da Zaitun na daga cikin kayayyakin Turai wadanda Amirka ta yi wa karin haraji mafi girma a dambarwar cinikayyar da ke tsakanin nahoyin biyu

https://p.dw.com/p/3RUtD
USA Georgia | Hafen von Savannah
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. B. Morton

Amirka ta yi karin kudin fito da kashi 25 cikin dari kan kayayyakin Turai da ake shigarwa cikin kasarta wadanda suka hada da  Barasa da Zaitun da Cikwi da sauransu.

Washington ta sanar da daukar matakin ne a matsayin martani dangane da rangwamen da kasashen Turai ke yiwa kamfanin kera jiragen sama na Airbus. 

Ta ce tana duba yiwuwar samun dala Biliyan bakwai da miliyan dari biyar daga karin kudin fiton.

Kungiyar ciniki ta duniya  WTO wadda ke shiga tsakani kan kasuwanci tsakanin kasa da kasa ta amince da  matakin karin harajin.