1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya ce FBI ta kai masa samame

August 9, 2022

Wasu majiyoyi a Amirka na cewa kotu ce ta sahale wa FBI din kutsawa gidan Donald Trump domin bincike ko ya boye wasu takardun sirri na gwamnati.

https://p.dw.com/p/4FIUY
CPAC-Konferenz in Texas | Donald Trump
Hoto: Brandon Bell/Getty Images/AFP

Tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya ce jami'an hukumar bincike ta FBI sun kai wani samame a wani katafaren gidansa da ke bakin teku a jihar Florida, yana mai siffanta lamarin a matsayin rashin da'a. Hukumar ta FBI dai ta kauce wa yin karin haske a kan samamen. To amma Trump wanda ba ya cikin gidan a ranar Litinin da daddare, a cikin sanarwar da ya fitar ya gaza fadin dalilin da ya sa jami'an suka ziyarci gidansa suka kaddamar da bincike. 

Jaridar New York Times ta ambato tsohon shugaban na zargin 'yan siyasar jam'iyya mai mulki ta Democrat da tura masa jami'an FBI domin su bankado wani abu da zummar goga masa kashin kaji, ya samu matsala, a takarar shugabancin  Amirka da yake honkoro a shekara ta 2024.

A watan Fabrairun da ya gabata rahotanni sun ce an gano akwatuna 15 makare da muhimman takardun gwamnati da Mr. Trump ya wuce da su gidansa maimakon ya bar su a Fadar White House.