Amirka da Rasha za su yi maganin kutse | Labarai | DW | 09.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Rasha za su yi maganin kutse

Kasashen Amirka da Rasha sun tattauna kan dabarun samar da wata cibiyar da za ta maganta barazanar kutse ta yanar Internet, musamman a kan zabe a nan gaba.

Shugaba Donald Trump wanda ya bayyana aniyar kasashen a wannan Lahadi ta shafinsa na twitter, ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnatinsa ke aiki da Rasha a shigen wannan tsarin.

Sakon na Donald Trump, na zuwa ne kwana guda bayan tozalin farko da ya yi da shugaba Vladimir Putin a taron manyan kasashe da aka kammala a kasar Jamus.

A cewar shugaban na Amirka bayan nace wa Putin da ya yi dangane da zargin kutsen zaben Amirka da ke kan Rasha, sun kuma yi magana da Putin din kan batun tsagaita buda wuta a kasar Syria, wanda ya ce samun hakan zai ceci rayuka masu yawa daga salwancewa.