Amirka da Iran sun yi musayar fursunoni | Labarai | DW | 16.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da Iran sun yi musayar fursunoni

Wani jami'i a gwamnatin Amirka ya tabbatar da musayar fursunoni tsakanin Amirka da Iran bayan da aka jima ana tattaunawa kan batu.

Jami'in wanda ya zabi a sakaya sunansa ya ce an saki Amikawa ne a wani shiri na musaya da bangarorin biyu suka amince da shi bayan da aka jima ana tataunawa a kansa.

Washington dai ta ce ta yi afuwa ga 'yan Iran din ciki kuwa har wanda ake yi wa shari'a da wanda aka rigaya aka yankewa hukunci har ma suka fara zaman jarun.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake gab da janyewa Iran takunkumin karya tattalin arziki da aka kakaba mata sakamakon shirinta na nukiliya wanda Tehran da kasashe yamma ke dab ta cimma daidaito a kansa.