Amirka da China a zargin satar fasaha | Labarai | DW | 19.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da China a zargin satar fasaha

China da Amirka sun sake musayar kalamai a hukumar kasuwanci ta duniya WTO a inda jakadan Amirka ya zargi China da satar fasaha yayin da jakadan China shi ma ya nuna yatsa ga Amirka a matsayin mai aikata wannan ta'asa.

Wannan cece-kuce na zuwa ne yayin da kasashe suka jeru suna suka ko ma kalubalantar tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Donald Trump na Amirka kan harkokin na kasuwanci yayin taron sake nazartar harkokin na kasuwancin duniya da ake yi daga lokaci zuwa lokaci karkashin hukumar ta WTO. A wannan rana ta Laraba ce dai ke zama rana ta biyu da ake zama na sirri kan kasar ta Amirka bayan zaman da aka yi a ranar Litinin.

Jakadan na Amirka dai Dennis Shea ya bukaci a mayar da hankali kan kasar ta China wacce ya ce akwai bukatar ta takure harkoki na masana'antunta kasancewar tana samar da kayayyaki marasa inganci da take jibgewa a kasashen ketare.