Amirka: An kama wanda ake zaton ya kashe Limamai | Labarai | DW | 16.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka: An kama wanda ake zaton ya kashe Limamai

Rundunar 'yan sandan birnin New York na Amirka, ta kama wani mutun da ake zargi da kisan Limamin wani masallaci da mataimakinsa a gundumar Queens.

USA Beerdigung Imam Maulana Alauddin Akonjee und Thara Miah

Gawawakin Limam Maulama Akonjee da maitaimakinsa Thara Uddin.

Mutumin da aka kama mai suna Oscar Morel mazaunin Brooklyn mai shekaru 35 da haifuwa, an kama shi da laifin kisan kai, tare da mallakar makami a cewar babban sifeton 'yan sandan birnin New York Hubert Reyes. A jiya Litinin ne dai aka gudanar da addu'o'i ga marigayi Imam Maulama Akonjee mai shekaru 55 da haifuwa da mataimakinsa Thara Uddin mai shekaru 64 da haifuwa, inda daruruwan mutane suka hallara a Brooklyn.

Musulman dai na birnin New York sun yi kira ga hukumomi da su dauki kwararan matakai domin basu kariya, tare da fatan ganin an hukunta duk wani mai hannu cikin wannan lamari.