1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aminu Maigari na NFF na hannun hukumomi

July 4, 2014

Bayan da Najeriya ta fita daga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, jami'an leken asiri sun yi gaba da shugaban Hukumar Kwallon Kafar kasar daga dawowarsa daga Brazil

https://p.dw.com/p/1CVvj
WM 2014 Achtelfinale Frankreich Nigeria
Hoto: Reuters

Da safiyar wannan Juma'ar ce 'Yan sandan farin kaya suka kai wani samame ofishin Hukumar Kwallon Kafar Najeriya wanda aka fi sani da Glass House da ke Zone 7 a Wuse Abuja.

Masu farin kayan sun isa ofishin ne da misalin karfe 11:30, makare a cikin wata mota kirar akori kura suna dauke da bindigogi.

Wannan na zuwa ne bayan da suka cafke shugaban hukumar kwallon kafar ta kasa wato Aminu Maigari shi ma da safiyar yau daga isowarsa daga Brazil, daidai lokacin da ya fito daga filin saukar jiragen saman Abuja na Nnamdi Azikwe. Inda Najeriya ta fita daga wasan cin kofin kwallon kafa na duniya, bayan da ta sha kashi hannu Faransa da ci biyu ba ko daya.

Idan ba a manta ba, ranar laraba ce, mai sharia Justice LP Lot na kotun Tarayyar dake zama a birnin Jos na Jihar Plateau ya dakatar da shugaban hukumar, Aminu Maigari da mambobin kwamitin gudanwarsa daga jagorantar harkokin kungiyar kwallon kafar kasar. Ya kuma bukaci Ministan harkokin wasanni Tammy Danagogo da

ya samar da shugaban hukumar na riko, kafin a cigaba da sharia. Haka nan kuma ranar alhamis, Ministan harkokin wasannin ya zabi Mr Lawrence Katken daya daga cikin mataimakan shugaban, a matsayin wanda zai rike wannan mukami kafin a yanke hukunci.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar