1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aminata mai sana'ar kayan lambu a Mali

Madelaine Meier/Zainab Mohamed/GATDecember 23, 2015

Aminata Niang wata matashiya ce, wadda gidansu ya yi fice a noman kayayyakin lambu. Wannan matashiya dai ta kan kai wadannan kayayyakin lambu zuwa kasuwa da kanta.

https://p.dw.com/p/1HSPz
DW Africa on the move Mali Aminata Niang
Hoto: DW

Noman kayan abinci domin amfanin ciki da wajen kasa na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kasashen Afirka ta Yamma musamman saboda karuwan bukatu. Alal misali kashi 80 daga cikin 100 na kayan lambu da ake ci a Accra da Bamako, ana nomansu ne a kewayen wadannan biranen. Aminata Niang wata matashiya ce, wadda gidansu ya yi fice a noman kayayyakin lambu. Wannan matashiya dai ta kan kai wadannan kayayyakin lambu zuwa kasuwa da kanta.

Matasa na shirya kokwamba da aka girbesu daga gonar su Aminata Niang, kafin a loda su a mota. Kayan lambun na bukatar kulawa ta musamman. Saboda haka ne manomiyar ta kasar Mali ke kokarin kaisu kasuwa cikin gaggawa don kada su lalace, inda matasan ke cusasu cikin akwatuna tare da sanyasu cikin mota.

"Mun kammala girbe kayan lambun. Za mu yi jigilarsu da yamma domin a lokacin ba a zafi sosai".

Aminata na zuwa kasuwanni domin sayar da kayan lambunta

DW Africa on the move Mali Aminata Niang
Hoto: DW

A matsayinta na kwararriyar mai fassara, da farko Aminata ba ta so shiga harkar kasuwanci ba. Sai dai a yau tana taka muhimmiyar rawa. Da kanta take daukar kayan lambu zuwa kasuwanni. A wannan karamar kasuwa da ke tsakiyar birnin Bamako, 'yan kasuwa na yin odar kayayyakinsu ne ta wayar tarho. Idan daya daga cikin masu cinikinta ya manta yin oda ta waya, to sai dai ya jira wanda ya rage bayan kowa ya karbi nasa..

"Wannan na wani abokin huldar kasuwanci ne. Don Allah ka barshi. Ba zan iya baka ba."

Aminata ta san masu cinikinta sosai. Dole ne a gwada nauyin kayayyakin sosai. Idan ba haka ba za'a cuceka, kamar yadda ta nunar...

"Sikelina ya sha banban da nata. Nata na da kankanta sosai. Akwai wata dabara da ‘yan kasuwa ke amfani da ita wajen ganin cewa sun ci riba sosai, mu kuma mu fadi. Saboda haka ne a ko da haushe muke jayayya da ita."

'Yan kasuwa na yabon dadin kan Aminata cikin huldar kasuwancinsu

DW Africa on the move Mali Aminata Niang
Hoto: DW

Duk da irin wannan jayayya, abokan kasuwancin Aminata ba sa daina hulda da ita. Domin tana da basira a tafiyar da harkar kasuwancinta, kana farashinta yana da kyau. Kamfaninsu yana da tsari mai inganci. Hakan ne ya sa har shekara ta kewayo gonarsu na samar da kukamba.

"Nethouse, wata dabara ce ta samar da yanayin da ya dace a gona. Kamar dai gidan sauro ne da ke kare shuka daga illar kwari da ruwan sama da kuma rashin kyawon yanayi."

Ba wani ba ne ke taimaka wa su Aminata illa mahaifinsu. Ya shafe shekaru 30 yana aiki a hukumar noma ta Majalisar Dinkin Duniya. Saboda hake ne yake taimaka musu da dabaru. Akan hakane Aminata ta ce, babu abin da za ta fada face godiya ga Allah saboda yadda mutanen gidansu ke aiki tare.

"Ina alfahari da su. Ko da an bani damar canza dangina da wasu, ban zan yi ba. Suna da fasaha da hadin kai."

Aminata da ke da matikar hakuri, ita ce daya daga cikin ‘ya’ya takwas da babanta ya haifa. Kuma a cewarta, suna muradin fadada gonarsu ta kayan lambu, domin kalubalantar dumbin bukatu da ke karuwa a Bamako.