Amfani kwallo kan kyautata rayuwa | Himma dai Matasa | DW | 26.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Amfani kwallo kan kyautata rayuwa

Wani dan kwallon kafa da ya yi wasa a kungiyoyin kasashen Turai Baky Koné, ya koma gida nahiyar Afirka dan horas da matasa da ke tasowa da sha'awar wasan kwallo cimma burin su. musamman a Abidjan.

Baky Koné, ya yi wasannin sa na karshe a biranen Paris da Katar, kamin ya yanke shawarar komawa gida. Ko da yake dai ba kowa ne ya fahimci niyar sa ba, amma ya cimma burin da matasa da dam,a ke muradi a rayuwa

Wannan ya sa wasu matasa ke cike da fata na taka leda a kasashen Turai. To sai dai babban kalubale da yawancin 'yan kwallo da ke wasa a nahiyar Turai shi ne samun takardun zama. Inda yawanci takardun zaman ya ta'allaka ne ga tsawon kontiragin da 'yan wasan ke da shi a kungiyoyin kwallon kafa da suke wasa.

Amma a yanzu sama da matasa 40 ne ke samun horo a wata makaranta ta musamman ba tare da biyan kudi ba. Oumar Diakite, guda ne daga cikin masu burin kammala karutu dan tsallakawa Turai.

Shi ma Ousseynou Zane, matashi ne da ke cike da burin tabbatar da haka ta cimma ruwa na zama gwarzon dan kwallo a duniya. Wannan ya sa yake ganin damar kasancewa cikin wannan makaranta ta horas da kwallaon kafa, wata dama ce ga rayuwarsa.

A yanzu dai akwai sama da matasa 3,000 da ke zama ba bisa ka'ida ba a wasu kasashen Turai musamman Faransa. Wannan ya sa Baky Kone, ke horas da wasannin kwallo ga dinbin matasa tare da ba su kwarin gwiwa da tsare mutuncinsu dan cimma burinsu a rayuwa.