Amfani da makaman guba a yakin Siriya | Labarai | DW | 09.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amfani da makaman guba a yakin Siriya

Rasha ta zargi 'yan tawayen Siriya da yin amfani da makamai masu guba akan fararen hula.

Wani sakamakon bincike da masana kimyya na kasar Rasha suka gudanar ya gano cewa, wani makami da aka harba a yankin Khan al-Assal dake kusa da birnin Aleppo na kasar Siriya, a ranar 19 ga watan Maris din da ya gabata na dauke da sinadarin Sirin mai guba.

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin, ya bayyana cewa a kwai kyakkyawan zato kan cewa 'yan tawayen Siriya ne suka harba shi.

Churkin ya ce harin da aka kai din ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 20, yana mai cewa kwararru daga kasar Rasha sun ziyarci gurin tare da gudanar da bincike wanda aka tantance binciken nasu a dakin gwaje-gwajen kimiyya na kasar ta Rasha da Hukumar hana yin amfani da makami masu guba a lokutan yaki ta amince da shi.

Mawallafiya : Lateefa Mustapha Ja'Afar
Edita : Saleh Umar Saleh