Amfani da jirage marasa matuka a Kwango | Labarai | DW | 03.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amfani da jirage marasa matuka a Kwango

Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar kaddamar da farmaki da jirage marasa matuka akan 'yan tawayen Kwango idan suka ci-gaba da tayar da kayar baya a gabashin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa zata kaddamar da farmaki kan kungiyoyin yan tawayen a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango, idan suka sake yin barazana ga zaman lafiya a gabashin kasar. Babban jami'in hukumar dake kula da kiyaye zaman lafiya Herve Ladsous ne yayi wanann bayani a birnin Goma, a lokacin da aka kaddamar da jiragen yakin nan marasa matuka a yankin Arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango.

Ita dai Majalisar Dinkin Duniya tana so ta yi amfani da wadannan jirage kirar Italiya domin dakile ayyukan tawaye musamman na 'yan kungiyar M23 a yankunan kasar Jamhuriyar Kwango. Wadannan jirage za a yi amfani da su wajen sa ido a kan zargin mara wa 'yan tawaye baya da ake zargin kasashen Ruwanda da Uganda da aikatawa, duk da musantawa da kasashen biyu suka yi.

A watan Maris na shekara mai kamawa ne ake sa ran fara aiki da wadannan jirage marasa matuka gadan gadan.

Mawallafi. Garzali Yakubu
Edita: Pinado Abdu-Waba