Amfani da addini don cin moriyar bunkasar matasa | Siyasa | DW | 12.09.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Amfani da addini don cin moriyar bunkasar matasa

Bayan share lokaci ana fuskantar rikici, hukumar kaiyade iyali ta duniya da manyan malaman addini da sarakai na wani zama a Najeriya da nufin lalubo hanyoyi na amfani da matasa ta hanyoyi da suka dace.

Kama daga bala'in ta'addar Boko Haram ya zuwa ga satar al'umma ta kasa da uwa-uba banga ta siyasa, Najeriya ta dauki lokaci tana ji a jiki sakamakon rigingimu iri-iri. Kuma cikin tsakiyar matsalar na zaman dimbi na matasa na kasar da ke da karfi na hatsi amma kuma suka koma 'ya'yan Iblis a cikin harkoki na rayuwar yau da kullum.

Matsalar kuma da ta dauki hankalin hukumar tsara iyali ta Majalisar Dinkin Duniya da tai kallon tsaf kuma ta tara sarakuna da ma manyan limaman addinin Musulunci da nufin muhawara da nemo hanyoyin sake dauke hankali na miliyoyin al'umma domin babban aikin ginin kasa a tsakaninsu.

Kuma ra'ayi ya banbanta kama daga masu tunanin kai karshen annobar fatara da samar da ayyukan yi ga matasan na iya kaiwa ga sauyin rawa da kila dora matasan bisa alkiblar daidai.

Bombenanschlag in Kaduna (AFP/Getty Images)

Matasa dai na tsaka mai wuya don gane da makoma a Najeriya

Fakewa a cikin addini da nufin cika burin son rai, batun na addinin dai na cikin tsakiyar kara yawan al'umma a sashen arewacin kasar da kila annoba ta talaucin ta mamaye yankin.

Sama da kaso 64 a cikin dari na 'yan kasar kusan miliyan 200 dai na zama na matasa, kuma kaso kusan 80 a dari na su ba su da aikin yi a tsakani na Musulman na arewa. Aliyu Shamaki dai na zaman daya a cikin matasan da aka gayyata ya zuwa taron kuma a fadarsa shekarun na tashi na zaman mafiya hadari ga rayuwa ta dan Adam cikin Najeriyar.

Tarrayar Najeriyar dai na  tsakanin neman cigaban al'umma amma kuma na fuskantar mummunan jahilci da rashin aikin yi a tsakanin miliyoyi na 'yan kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin