Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuka a Nepal
July 7, 2024Talla
Kakakin rundunar 'yan sandan Nepal, Dan Bahadur Karki ya ce har yanzu ana ci gaba da neman wasu mutane tara da suka yi batan dabo a sassan kasar. A cewarsa, tawagarsa na gudanar da ayyukan ceto a yankunan da iftila'in ya shafa. Hukumar Kula da Yanayi ta kasar ta yi gargadin cewa, wasu sassan kasar za su ci gaba da fuskatar saukar ruwan sama mai karfi da kuma tsawa har zuwa gobe Litinin.
Tun a farkon watan jiya ne, iftila'in sakamakon mamakon ruwan sama da kuma walkiya ya yi sanadin rayukan mutane 50 a kasar ta Nepal.