Ambaliyar ruwa ta yi barna a Najeriya | Duka rahotanni | DW | 10.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Najeriya

Fiye da mutane 11 ne suka mutu a garin Suleja da ke jihar Neja a sakamakon ambaliyar ruwa mai karfin gaske da ya kuma haddasa asarar dukiya.

Überschwemmungen in Westafrika (picture-alliance/ dpa)

Masu aikin ceto sun yi ta kokarin ceto jama'a a unguwar Chechenya daya daga cikin yankunan da wannan bala'i ya shafa a garin  Suleja a jihar Neja da ke kuma makwabtaka da Abuja babban birnin Kasar. Ruwan sama  Kamar da bakin kwarya ya yi dalilin afkuwar ambaliyar ruwan  da ya haifara da wannan barna da a Hausawa kan ce ruwa ya yi gyara.

FLASH-GALERIE Symbolbild Überschwemmungen Westafrika (picture alliance/dpa)

Daga cikin  gidaje zuwa ga kayayyakin jama'a har ma da motoci sun zama tamkar yadda iska ke daukar leda haka ruwan sama da ya yi ambaliya ya haifar da mummunar  damuwa a tsakanin al'umma, wasu yankunan garin na Suleja, baya ga gine-gine da ruwan sama ya hada rushewarsu. Malam Sulaiman Nuhu mazaunin unguwar Chechenya  da ke Suleja  ya bayyana  irin barnar da ruwan ya yi masu. Tun kafin faduwar daminar  bana, Hukumar Hasashen Yanayi ta yi gargadin cewa za'a samu ruwa mai yawa a bana da zai sauka a lokaci guda da fatan mahukunta za su dauki mataki.

Ana dai ci gaba da ambato alkaluma na yawan mutanen da suka mutu daga 11 inda wasu kafofin yada labaran ke bayyana cewa sun zarta hakan, saboda rashin samun cikakken adadi na gwamnati. Bayanai na nuna cewa fiye da shekaru 20 kenan rabon da a ga ambaliyar ruwa irin wannan a garin na Suleja da ke jihar Neja, a sauran sassan kar ma dai an sami  ambaliyar ruwan  a birnin Lagos al'amarin da ya kai ga tafka asarar dukiya da kuma tsayar da hada-hadar kasuwanci a jahar. A shekara ta 2012 ne Najeriya ta gamu da ambaliyar ruwa da ta fi muni a ‘yan shekaraun nan wacce ta yi dalilin mutuwar mutane 363 tare da raba wasu akalla miliyan daya da rabi da muhallansu.

Sauti da bidiyo akan labarin