Ambaliyar ruwa ta ritsa da yankin Balkan | Labarai | DW | 18.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa ta ritsa da yankin Balkan

Kusan mutane 30 sun hallaka bisa ambaliyar ruwa da aka kasashen Bosniya da Sabiya, inda wasu sama da 20,000 suka rasa gidajensu

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka a kasashen Bosniya da Sabiya ya yi sanadiyar hallaka mutane kusan mutane 30, yayin da mahukuntan suka kwashe kimanin kauyawa dubu 16 daga gidajensu, wadanda suka fuskanci ambaliyar ruwa.

Mahukuntan Sabiya sun nemi mutane su yi taka tsantsan da aiki da wutar lantarki, saboda yanzu haka ambaliyar ruwan ta raba mutane dubu 78 da hasken wutar lantarki, sannan mutane dubu 60 suka rasa wutar lantarkin a Bosniya. Zabtarewar kasa kuma ta lalata gidaje masu yawa. Inda ministan kula da yan gudun hijira na kasar Bosniya Adil Osmanovic, ya ce yanzu muta ne kimanin 20,000 malalar ruwan ya tilastawa barin gidajensu.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Usman Shehu Usman