Ambaliyar ruwa ta ritsa da dubban mutane | Labarai | DW | 22.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa ta ritsa da dubban mutane

Ambaliyar ruwa ta hallaka fiye da mutane 500 a Indiya, sannan ana neman ceto dubbai.

Masu aiki ceto na kasar Indiya na ci gaba da neman dubban mutanen da ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa ta ritsa da su cikin yankin arewacin kasar. An tabbatar da mutuwar mutane fiye da mutane 500.

Hukunomin sun samu nasarar kwashe kimanin mutane dubu 70, bayan hasashen masana na shatata ruwa na tsawon kwanaki biyu, kuma yanzu haka akwai kimanin mutane dubu 50 da suka makale cikin yankin na arewacin kasar.

Kawo yanzu akwai kimanin mutane dubu 10 da suka bace cikin mabaliyar ruwa da ta ritsa da kasar ta Indiya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman