Ambaliyar ruwa ta hallaka sama da mutum 500 a Chadi
September 22, 2024Talla
Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa ta'adin ambaliyar ya shafi kimanin mutum miliyan daya da dubu 700, inda gidaje sama da dubu 200 ne suka lalace.
Ambaliyar ta kuma lalata sama da gonaki da suka kai hekta dubu 880 a Chadin, a cewar ofishin da ke kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA da ke a kasar.
Dukkanin lardunan kasar dai sun taɓu da ibtila'in, inda kuwa har ya zuwa yanzu hukumomi ke gargadin iya fuskantar ambaliyar a bana.
A farkon wannan wata na Satumba ma dai Majalisar Dinkin Duniyar ta ja hankali a game yiwuwar samun ruwan sama mai yawa a musamman Chadi da kewaye, abin kuma da ke da alaka kai tsaye da sauyin yanayi da duniya ke fuskanta.