SiyasaAfirka
Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 341 a Chadi
September 10, 2024Talla
Ofishin kula da jinkai na MDD ya ce ambaliyar ruwan ya shafi larduna 23 na kasar ta Chadi. Kazalika gidaje sama da 164,0000 suka lalace tare da asarar shanu sama da dubu 70,000.
Karin bayani: Ambaliya ta yi barna a Chadi
Har yanzu dai hukumomin kasar ta Chadi ba su fitar da alkaluman wannan ibtila'i ba, wanda ko a makon da ya gabata ambaliyar ruwan ta halaka wasu daliba 14 tare da malaminsu a yankin Ouadda da ke shiyyar gabashin kasar. Wasu rahotannin sun bayyana cewa mutane 54 sun mutu a lardin Tibesti da ke da tsakiyar sahara a arewacin kasar sakamakon mamakon ruwan sama.