Ambaliyar ruwa ta haifar da asarar rayuka a kasar Sin | Labarai | DW | 11.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa ta haifar da asarar rayuka a kasar Sin

Mutane 66 ne suka rasa rayukan su a kudancin kasar sin, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya. Ambaliyar ruwan ta kuma haifar da hijirar wasu mutane kusan dubu dari 6. Har ila yau ruwan saman ya kuma lalata gidajen kwana na mutane kusan dubu 50 a larduna uku da al´amarin ya shafa.Kamfanin dillancin labaru na kasar Xinhua ya kuma tabbatar da bacewar wasu mutane 12. Rahotanni dai sun shaidar da cewa har yanzu, ana nan ana ci gaba da gudanar da ayyukan agaji a yankin da wannan abu ya faru.