Ambaliyar da ta rutsa da kudancin Asiya | Siyasa | DW | 30.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ambaliyar da ta rutsa da kudancin Asiya

Dubban Jamusawa na daga cikin wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a kudancin Asiya

Kusan akullu-yaumin, tun bayan afkuwar wannan bala’i daga Indallahi sai an tsinci gawawwakin dubban mutane, abun dake bayyana irin barnar da masifar ta haddasa da kuma mawuyacin halin da aka shiga ba ma a kasashen dake gabar tekun Indiya ba, har da sauran sassa na duniya. Wannan masifar tana mai amsa sunanta ne na kasancewa gama duniya, inda ake ci gaba da lalube domin binciko karin mutanen da aka rasa makomarsu, a baya ga fargabar da ake yi na yaduwar annoba a yankin kudancin Asiya. Wani abin lura game da masifar dai shi ne yadda ta dada kusantar da sassan duniya da juna, inda kusan dukkan kasashe suka tashi tsaye domin ba da taimako gwargwadon ikonsu. Ita ma Jamus bata yi wata-wata ba wajen gabatar da nata taimakon nan take. Shugaban gwamnati Gerhard Schröder ya ware tsabar kudi Euro miliyan 20 domin taimakon gaggawa tare da ba da sanarwar sarara wa kasashen Indonesiya da Somaliya bashin dake kansu har ya zuwa wani lokaci nan gaba. Kiran da shugaban gwamnatin na Jamus yayi ga jama’ar kasar da su yi wa Allah da Ma’aiki su ba da gudummawar kudi abu ne dake yin nuni da yadda gwamnatinsa ta damu da halin da ake ciki a yankunan da bala’in ya rutsa da su. A lokaci guda kuma gwamnatin na bakin kokarinta wajen ganin an kwaso Jamusawa dake yawon bude ido a wadannan yankuna zuwa gida ba tare da wani dogon turanci ba. Amma abin mamaki shi ne yadda wasu daga cikin Jamusawa masu yawon bude idon ke korafi a game da wai kayansu da suka bata ko kin kula da makomarsu daga bangaren kamfanonin yawon shakatawa. Wannan ba kome ba ne illa tsabar son kai da rashin sanin ya kamata da kuma watsi da mawuyacin halin da mazauna yankunan bala'an suke ciki. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda shugaban gwamnati Gerhard Schröder yake wa masu korafin hannunka-mai-sanda da cewar Jamus fa kasashe dake da wadatar arziki matuka gaya fiye da sauran kasashen da bala’in ya shafa. Akalla dai ba za a hadu a lalace ba. Domin kuwa an samu wasu daidaikun mutane a tsakanin masu yawon bude idon da suka nuna karimci da sanin ya kamata suna masu shiga gadan-gadan ana damawa dasu a matakan taimakon sauran jama’ar da bala’in ya rutsa dasu. Mutanen dake bukatar taimakon gaggawa daga gwamnati a tsakanin Jamusawa sune wadanda suka yi asarar iyaye ko ‚ya’ya da sauran danginsu sakamakon wannan tsautsayi. Abin fata kuma shi ne ba za a yi watsi da makomar kasashen da lamarin ya shafa bayan sun daina shiga kanun labarai ba. Kasashen Turai na da rabonsu na alhakin taimakawa wajen kyautata makomar wadannan yankuna, wadanda aka yi shekara da shekaru, suna ya da zango a cikinsu domin shakatawa.