Ambaliya ta yi sanadiyar mutuwar mutane 200 a Sudan da Senegal | Labarai | DW | 11.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya ta yi sanadiyar mutuwar mutane 200 a Sudan da Senegal

Ambaliyar ruwan sama da ake ci gaba da samu a kasashe Afirka ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari biyu yayin da ya raba wasu akalla mutum miliyan guda da matsugunnansu a kasashen Senegal da Sudan.

Ofishin da ke kula da ayyukan jin kai na MDD na ganin a wannan shekarar bukatar agajin gagawa zai rubanya na shekarar da ta gabata a sabili da yadda ruwan ke ci gaba da yin barna. 

Kasashe goma sha daya ne ke fama da ambaliya a kasashen yammacin Afirka da ma kasashen taskiyar nahiyar ciki kuwa harda Najeriya da Nijar. 

Firai Ministan kasar Nijar Brigi Rafini a wata ganawa da ya yi da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen ketare da wasu jakadun kasashen waje ya nemi a taimaka wa Nijar kasancewar girman barnar a kasar. Mutum saba'in da daya ne suka mutu yayin da ambaliyar ta shafi mutane dubu dari uku da hamsin.