1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ambaliya ta kashe rayuka a Indiya

July 24, 2021

Masu aikin ceto a Indiya, na can suna ta kokarin ganin yadda za su iya ceto wadanda ke da sauran numfashi a yankunan da ambaliya ta yi wa barna.

https://p.dw.com/p/3xzG7
Erdrutsche in Indien
Hoto: National Disaster Response Force/AP/picture alliance

Masu aikin ceto a Indiya, na can suna ta kokarin ganin yadda za su iya ceto wadanda ke da sauran numfashi a yankunan da ambaliya ta yi wa barna, inda rahotanni ke cewa sama da mutum 100 ne suka mutu.

Bayanai dai na cewa an yi nasarar ceto sama da mutum 900 kawo i iyanzu, a ambaliyar da ta auku a yankin yammcin kasar da ya fuskanci ruwan sama kamar da bakin masaki.

Daruruwan mutane ne suka rasa muhallansu a yankin Goa da ke kusa da Mumbai babbar cibiyar kasuwancin kasar ta Indiya, barnar da aka ce an kwashe gomman shekaru ba ga irin ta ba.

Sama da rabin wadanda suka salwanta a cewar masu aiko da rahotanni, sun fito ne daga yankin Raigad da ke kudancin birnin na Mumbai.