Ambaliya a Philippines ta halaka mutane 130 | Labarai | DW | 23.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliya a Philippines ta halaka mutane 130

Wadanda ambaliyar ta shafa na zaune ne a kudancin tsibirin Mindanao mai mutane miliyan 20 da ba kasafai ake ganin irin wannan bala'i ya afka masa ba kamar sauran wurare, a cewar jami'an Philippines .

Mutane da suka halaka sakamakon ambaliyar ruwa da kwararar yumbu da ke zuwa ta sanadin ruwa sama mai karfin gaske hadi da guguwa mai lakabin Tembin a Kudancin Philippines ya yi sanadi na rayukan sama da mutane 130 kamar yadda jami'an 'yan sanda da wadanda ke sa ido kan afkuwar bala'i suka bayyana a wannan rana ta Asabar.

A cewar jami'an wadanda abun ya shafa na zaune ne a kudancin tsibirin Mindanao mai mutane miliyan 20 da ba kasafai ake ganin irin wannan bala'i ya afka masa ba kamar sauran wurare da ke ganin irin wannan a kusan duk shekara. 'Yan sanda da sojoji da masu aikin agaji na ci gaba da zakulo mutane daga inda yumbu ya rufesu yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace a garin Dalama a wannan Asabar.

Kogi ya tumbatsa ya yi gaba da gidaje a kauye kusa da garin Tubod kamar yadda Gerry Parami jami'in 'yan sanda a yankin ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.