AMBALIYA A KUDANCIN ASIA. | Siyasa | DW | 03.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AMBALIYA A KUDANCIN ASIA.

Harkoki sun fara daidaita ,bayan ambaliyan ruwa daya ritsa da kasashen kudancin Asia,a tsakiyan watan Yuli.

Ambaliya a Bangladash.

Ambaliya a Bangladash.

Bayan lokaci mai tsawo ana fafutukan shawo kann ambaliyan ruwa daya kashe kimanin mutane 1,350 a yankin kudancin Asia,masana sun bayyana cewa a halin yanzu komai ya fara lafawa.

Sai dai a hannu guda kuma hukumomin kasar zasu fuskanci matsaloli wajen agazawa mutanen da wannan ambaliya ya ritsa dasu,tare da sake tsunar dasu,banda gine ginen gwamnati da suka salwanta.

Rahotanni hukumar bada agajin abinci ta mdd tayi nuni dacewa ,a Bangladash kadai,ambaliyar ta haddasa asara kwatankwacin dalan Amurka billion 7.Hukumar tace a wannan ambaliya daya ritsa da yankin tun daga tsakiyan watan yulin daya gabata,ya lalata gidaje,da gonaki,tare da dabbobin Jamaa.

Wakilin hukumar a birnin Dhaka Douglas Casson,yace gonaki da dama sun salwanta,kuma daga yanzu zuwa watan Afrilu ne ake saran fara girbin Shinkafa a kasar Bangladash.

Sai dai ya bayyana cewa a yanzu haka hukumarsa ta dauki nauyin tallafin shinkafa acikin kasar wa kimanin mutane million 1.8,tare kuma da kira ga kungiyoyin agaji dasu taimakawa jamaar yankin.

Ministan kula da harkokin da agaji na Bangladash Kamal Ibn Yusuf,yace gwamnati na taimakawa jamaa da kayayyakin abinci da magunguna,a sassa daban daban na kasar.Yace suna isassun abinci da magunguna da zasu kalubalanci yanayin,domin zasu iya ciyar kimanin mutane million 20 ,daga yanzu har zuwa watan maris na shekara mai zuwa.

Sai dai Ministan ya koka da irin matsaloli da ake fuskanta wajen rabon kayayyakin na agaji.

A nata bangare hukumar asusun tallafawa kananan yara ta UNICEF,ta kaddamar gidauniyar neman taimako na dala million 13 da dubu dari 4 ,ranar litinin domin taimakawa mata da kananan yara da magunguna,a yankunan da ake fama da amai da gudawa sakamakon gurbataccen ruwa.

Hukumar inganta rayuwa ta Amurka watau USAID a takaice tayi alkawarin bada tallafin dala dubu 960,akan dubu 60 da a farko ta sanar da bayarwa.

Ambaliyan dai ya bar sama da mutane million 21,babu matsuguni ,wanda ya kasance mafi munin irinsa a yankin kudancin Asia a yan shekaru da suka gabata.

Zainab Mohammed.