1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Amazons: Dakaru mata zalla a daular Dahomey.

Rodrigue Guezodje
February 20, 2021

Ficen da masarautar Dahomey, tsakanin karni na 17-19, da a yau ake kira Jamhuriyar Benin, ya samu ne saboda kafa wata rundunar mayaka da ta kunshi mata zalla, wadanda aka kira ''Dahomey Amazon''.

https://p.dw.com/p/3peFw
African Roots | Dahomey-Amazonen | Porträt

Yankin Dahomey wanda ke a kasar da ake kira Benin a yau, yanki ne mai dumbin tarihi dag cikin masarautun gargajiya a nahiyar Afirka inda sarakuna 15 a jere suka yi ta maye juna. Sai dai da wuya ne kundayen tarihin wannan masarauta ke bayyana wata jarumar mace da ta yi mulkin shekaru uku. Matan dai kan taka rawa a lokuta da dama, kamar yadda ta tabbata a tarihin jagorancin wannan kasa.

Wace ce sojar farko ta masarautar Dahomey?

A cewar masanin tarihi Bienvenu Akoha, Tassi Hangbe, 'yar Sarki Houegbadja, wanda ya samar da masarautar Dahomey, ita ce mace ta farko a rundunamra mayaka mata zalla da Dahomey. Kuma ita ce 'yar uwar tagwaitakar Sarki Akaba. A shekara ta 1708 ne dan uwan tagwaicinta wato Sarki Akaba, ya mutu bayan wata jinya. An dora ta a asirce a kan madafun ikon rundunar mayakan kasar, sannan kuma bayan komar su gida, aka tabbatar da ita a matsayin Sarauniyar Dahomey.

African Roots | Dahomey-Amazonen

Ta ina Tassi Hangbe ta taiamaka wa mutane a zamaninta?

Duk da cewar sarautarta ba ta wuce ta shekaru uku kacal ba, Tassi Hangbe, ta samu lokaci sosai wajen bayar da hankali ga mata. Ta sanya su harkokin da maza ne zalla ke yi , irin su farauta da noma da kiwo. Ta karfafa harkokin noma sosai da kuma tabbatar da samar da ruwan sha a wadace ga talakawanta.

Ta yaya ne mayakan Dahomey Amazons suka bambanta da saura?

 

Da yake Tassi Hangbe ta yi saurin fahimtar cewa da wuya ne ta gudanar da abubuwan da take so, sai ta kafa wata bataliya ta mayaka mata zalla. Zaratan matan da aka kira Agoodjie a harshen Fon (wanda ke nufin dogarawa na kuda da Sarauniya) mata ne da ake ba su horo tun suna kanana. Wannan horon ya kuma sanya su masu matukar jarunta fiye da maza. A lokacin yaki ba su da tausayi sam, har ma suna iya fille wa duk wani da ya yi kokarin turje wa abin da suka sanya a gaba.

Wasu gwamman shekaru bayan Sarauniya Tassi Hangbe, Sarki Guézo ya mulki masarautar Dahomey. Ya kuma yi saurin fahimtar fa'idar kasancewar wadannan mayaka mata a tare da shi, mayakan da zakakurar mace, Seh Dong Hong Beh (Sê do Houngbé cikin harshen Fon) ta jagorance su. Suna kawo wa sarkin fursunonin da ake mika su ga dillalan kasar Brazil inda ake musanya su da makamai da taba sigari da kuma barasa. Wancan fataucin mai dan karen kudi, shi ne ya sama wa masarautar Dahomey karfi a wancan zamani.

African Roots | Dahomey-Amazonen

Wane tarihin rundunar ta mata ta Dahomey Amazons ta bari?

A shekara ta 1882, Sarki Behanzin, wanda ya yi kokarin kare hakkin cinikayya da kaddamar da yaki da kasar Faransa. Sai dai saboda karfin makamai da sojojin Faransa ke da shi, wadannan mata mayaka na Amazons suka kwashi kashinsu a hannu; domin an kashe su da dama. Duk kuwa da aikata a bainda a zamanin yau ake kira laifukan yaki, har yanzu ana kallon mayakan mata zalla a matsayin wata alama ta wasu da suka zama ceto mata. Bayan kuma matuwa da su da aka yi tsawon shekaru, sannu a hankali ana karrama su.  An gina wani gidan tarihi na Abomey,  saboda Sarauniya Tassi Hangbe. Ko bayan wannan ma, har yanzu akwai wasu da ke da nasaba da tsatson Sarauniyar wadanda ke bukukuwan tunawa da ita, inda suke wake-wake da kuma raye-raye.

Wannan makalar ta samu ne tare da taimakon masana tarihi, irin su; Farfesa Doulaye Konaté da Farfesa Lily Mafela da kuma Farfesa Christopher Ogbogbo. Shirin Tushen Afirka dai na samuwa ne tare da tallafin gidauniyar Gerda Henkel.