Al′ummar Tunisiya na zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 21.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Tunisiya na zaben shugaban kasa

Al'ummar kasar Tunisiya sun fita kada kuri'a domin zaben sabon shugaban kasa a zagaye na biyu a wani abu da ke nuna sabon salo bayan juyin-juya hali a shekara ta 2011.

Zagaye na biyu na zaben tsakanin 'yan takara biyu na kasancewa zabe na karshe a watanni biyu da suka gabata kuma zai kasance na karshe a kokarin da kasar ke yi na sauya tafiyarta bisa tafarkin dimokradiya tun bayan juyin-juya hali da ya kunno kai a tsakanin kasashen Larabawa wanda ya yi awun gaba da mulkin tshohon Shugaba Zine El Abidine Ben Ali.

Masu fafatawar Beji Caid Essebsi, dan shekaru 88 tsohon minista a gwamnati da ta shude, na bugawa da Moncef Marzouki dan fafutukar hakkin dan Adam wanda kuma ya rike Firayim Minista a gwamnatin rikon kwarya bayan juyin juya hali a kasar.

A lokacin da ya je kada kuri'arsa Hatem Dekali wani ma'aikaci a kamfanin zirga-zirgar jiragen sama a kasar ya ce: "Abu ne da ke da kyau a yanayin da ake zaben domin ba wanda ke da tabbacin wanda zai yi nasara sai an kammala an bayyana sakamako sabanin lokutan baya".

Cikin dai kasashen da suka shiga fafutikar kafa mulkin dimokradiya kasar dai ta Tunisiya har yanzu ta ci gaba da tafiya bisa hanyar da ake tsammani. Sama da mutane miliyan biyar suka cancanci kada kuri'a wannan zabe.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo