1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'ummar Togo sun yi nisa a kada kuri'un zaben shugaban kasa

April 25, 2015

Shugaba Faure Gnassingbe ya jefa kuri'arsa a birnin Lome fadar gwamnatin kasar da safiyar wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/1FEoz
Faure Gnassingbe bei der Abgabe seines Stimmzettels zur Parlamentswahl in Togo am 25.07.2013
Faure Gnassingbe shugaban kasar TogoHoto: Reuters/Noel Kokou Tadegnon

Al'ummar kasar Togo na ci gaba da kada kuri'arsu a zaben shugaban kasa a wannan kasa da ke a yammacin Afrika, kasa da ke klarkashin mulkin iyali guda kusan shekaru hamsin.

Shugaba Faure Gnassingbe ya jefa kuri'arsa a birnin Lome fadar gwamnatin kasar da safiyar Asabar dinnan . Mahaifi ga shugaba Gnassingbe dai ya mulki wannan kasa tsawon shekaru 38 har sai a shekarar 2005 da ya mutu sakamakon cutar bugun zuciya. Tun a wancan lokaci ne shugaba mai ci ya dare karagar mulkin kasa daga bisa aka sake zabe inda anan ma ya sake nasarar ci gaba da kasancewa kan karagar mulki.

A shekarar bara 'yan majalisar dokokin kasar sun gabatar da wani kudirin doka da ke da nufin ganin an takaita zangon wa'adin mulkin shugaban kasa ya tsaya tsawon zango biyu kawai sai dai kudirin dokar ya gaza samun nasara.

Kimanin masu sanya idanu daga kasashen waje 500 ne za su ga yadda zaben zai gudana a mazabu sama da 4,000 inda mutane miliyan uku da dubu dari biyar za su kada kuri'unsu, wato kimanin rabin adadin mutanen kasar miliyan shida da dubu dari takwas.