Al′ummar Musulmin duniya sun soma Azumin watan Ramadan | Labarai | DW | 27.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Musulmin duniya sun soma Azumin watan Ramadan

A wannan Asabar din ce Musulmi a sassa daban-daban na duniya suka tashi da Azumin watan Ramadan bayan ganin jinjirin wata da ke nuni da karshen watan Sha'aban, kuma farko watan Ramadan.

Symbolbild Ramadan (picture-alliance/dpa/N. Mounzer)

Shaidar jinjirin Watan Ramadan

A kasashe da dama na Musulmi, irin su Jamhuriyar Nijar, da Tarayyar Najeriya al'umma sun tashi da azumi a wannan rana ta Asabar, bayan da majalisun koli na addinin Musulunci na kasashen suka tabbatar da ganin jinjirin wata.

A jawabin da ya yi wanda kuma wakilinmu na Sakkwato Faruk Mohammed Yabo ya aiko mana, mai martaba Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar na III da ke a matsayin shugaban majalisar Muslunci ta Tarayyar Najeriya ya yi kira ga jama'a Musulmi da su tashi da Azumin na Ramadan a wannan rana ta Asabar da ke a matsayin ranar daya ga wata.