Al′ummar Kirista sun fara bukukuwan Easter a duniya | Labarai | DW | 18.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'ummar Kirista sun fara bukukuwan Easter a duniya

Mabiya addinin Kirista a fadin duniya sun fara gudanar da bukukuwan Easter, tun a cikin dare ne bikin ya kankama a fadar Vatikan da ke birnin Rom.

A cikin daren dai Fafaroma Francis ya bukaci manyan limaman cocin Katolika da su kaurace wa kyale-kyalen duniya inda dukanninsu suka sake sabunta rantsuwar kama aiki da suka yi a lokacin da aka zabe su. A taron addu'oin da Fafaroman ya gudanar wanda akalla mutane 10,000 suka halarta ya yi huduba inda ya bukaci manyan limaman Coci da su rinka gudanar da rayuwa mai sauki. Ya kuma ce dole ne Cocin Katolika ta kasance wani wajen samun mafaka ga mabukata yayin da daga bisani ya wanke kafafuwan nakasassu 12 a wani bangare na al'adun da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis da daddare wato jajiberin bukukuwan na Easter. Za dai a ci gaba da bukukuwan har zuwa kwanaki uku masu zuwa inda za a ci gaba da yin addu'oi da shagulgula daban-daban. Easter na daya daga cikin bukukuwa masu muhimmanci a cikin addinin Kirista.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal