Al′umma sun kadu da zaben gaggawa a Birtaniya | Siyasa | DW | 18.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Al'umma sun kadu da zaben gaggawa a Birtaniya

Wannan mataki dai na zama ba zata ga daukacin 'yan kasar, amma Firaminista Theresa May ta ce za ta yi amfani da damar dan jan hankalin majalisa wajen mara wa kudirin baya.

Al'ummar kasar sun ji labarin ba zata, a sanawar da Thereasa May ta fitar kan ranar sabon zaben ganin yadda akasarin jam'iyyun adawa a Birtaniya ke fama da matsalolin cikin gida, 'yan kasar na ganin wannan zaben zai kasance tamkar wanda aka gani lokacin kuri'ar ballewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Tun dai lokacin da Firaminista Theresa May ta dare shugabancin  firaminista a kasar, bayan murabus din David Cameron bayan zaben raba gardama a watan Yunin bara, ake rade-radin kiran zabe gabanin lokacinsa, amma May ta yi ta musunta yiwuwar hakan. Ko da a watan Satumba an rawaito ta na cewa ba zan taba kiran zabe gabanin lokacinsa ba, sai dai May ta bada hujjar da a yanzu ya sa ta ta kira zaben.

"A 'yan kwanakin nan jam'iyar Labour ta yi barazanar kada kuri'a bisa yarjejeniyar da muka yi. Jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi suna barazanar tsayar ayyukan gwamnati cak,  Jam'iyyar 'yan Scotland ta ce za ta kada kuri'ar sauya kudurin da muka yi wanda a hukumance ya ayyana ballewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, wakilan babbar majalisa da ba zabensu aka yi ba, sun dukufa don yakarmu ta ko wace hanya, idan har bamu gudanar da zabe a yanzu ba, to za su cigaba da yawo da hankalinmu. Kana batun ficewarmu  daga Kungiyar Tarayyar Turai zai kasance da matsala in muka jira lokacin da aka shirya gudanar da zabe." 

Ko da yake firimiyar ta Birtaniya ta bada hujjujinta, amma ga 'yan Birtaniya dayawa hakan yazo musu a bazata. Farfesa Steven Fielding  shi ne daraktan cibiyar siyasa a jami'ar Nottingham. DW ta tambayeshi ko shi ma ya ji mamaki da sanawar ta Thereasa May:

"Eh abun ya zo min da mamaki, haka kuma ga dukkan jama'a in baya ga wadanda ke fadar gwamnati, domin mintuna 30 kafin sanarwar ne kawai 'yan jarida suka ji alamar za'a yi bayani kan zaben, don haka an yi matukar boye maganar. Abin da ya kara baiwa mutane mamaki shi ne, yadda Theresa May ta yi ta nanata ko da yaushe, kan cewa ba za ta kira sabon zabe ba."

Wani abun da masana ke cewa shi ne dalilin Thereasa May ta sauya ra'a yi ta kira zabe a yanzu shi ne, yadda jam'iyarta ke da rinjaye bisa alkaluman ra'ayin jama'a, kuma ita kanta firaministar, farin jininta ya na matukar tashe tsakanin al'ummar Birtaniya, inda ake yi mata kallon wacce kan iya zaburar da tattalin arziki, idan aka kwatanta da Jeremy Corbyn shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Labour. 
 

 

Sauti da bidiyo akan labarin