Al′umma a Masar sun fita zaɓen ′yan majalisa | Labarai | DW | 18.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Al'umma a Masar sun fita zaɓen 'yan majalisa

Ana ta cece-kuce sakamakon kaka-gidan da 'yan takarar jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak da juyin- juya-hali ya kawar da su, suka yi.

Bahrain Botschaft Ägypten Wähler Wahlen

Zaben 'yan majalisa ya kankama a Masar

A ranar Lahadin nan al'ummar ƙasar Masar za su fita kaɗa ƙuri'a a zaɓen 'yan majalisar dokoki a karon farko tun bayan hambarar da gwamnatin 'yan uwa Musulmi ƙarƙashin jagorancin Mohammad Morsi fiye da shekaru biyu ke nan. Zaɓen da jam'iyyun adawa ke ƙauracewa, kuma ana ta cece-kuce a kansa sakamakon kaka-gidan da 'yan takarar jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Hosni Mubarak da juyin- juya-hali ya kawar da su suka yi.

An dai a buɗe tashoshin kaɗa ƙuri'a a yankunan gwamnoni 14 daga cikin 27 na ƙasar ta Masar a zagayen farko na zaɓen da za a ɗauki kwanaki biyu ana yi da nufin neman kujeru 286 wanda 'yan takara sama da 2000 za su fafata.

Tun daga ƙarfe tara ne dai agogon ƙasar za a fara zaɓen wato ƙarfe bakwai agogon GMT. Sannan a tsammaci fitar sakamakon zaɓen da ke zama kashin farko ranar 30 ga watan nan na Oktoba.