1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umar Togo na zaben shugaban kasa

February 22, 2020

Al'umar kasar Togo na can suna kada kuri'a, a zaben shugaban kasa da ake yi a yau Asabar, zaben da ake ganin zai bai wa Shugaba Faure Gnassingbe dama karo na hudu.

https://p.dw.com/p/3YBrz
Togo Präsidentschaftswahl in Lome l  Wahllokal
Hoto: Reuters/L. Gnago

Shugaban kasar Faure Gnassingbe mai shekaru 53, na jagorantar kasar da ke yammacin Afirka ne tun cikin shekarar 2005, bayan mutuwar mahaifinsa, Gnassingbe Eyadema, wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 38.

Masu kada kuri'a sun fito tun da jijjifin safiyar Asabar a Lome fadar gwamnati, inda da dama daga cikinsu suka bayyana fatan ganin sauyi a siyasar kasar.

A shekara ta 2017 ne dai iyalan Gnassingbe suka fuskanci adawa daga 'yan kasar da suka bukaci kawo karshensu a mulki da suka kwashe shekaru 50 suan yi.