Alpha Conde na kan hanyar lashe zabe a Guinea | Labarai | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Alpha Conde na kan hanyar lashe zabe a Guinea

Sakamakon wucin gadi da hukumar zaben kasar ta Gini ta wallafa yammacin jiya Laraba ya nunar da cewa Shugaba Alpha Conde na a sahun gaba da gagarimin rinjaye.

Sakamakon wanda ya shafi a halin yanzu kashi daya daga cikin hudu na kuri'u miliyan shida da aka kada, ya nunar da cewa Alpha Conde ya lashe zaben a gudumomi 10 daga cikin 38 musamman a yankunan tsakiyar gabashi dama a kudancin kasar.

Amma madugun 'yan adawa Cellou Dalein Diallo ya samu babban kaso a yankunan tsakiya da ke a matsayin cibiyar 'yan adawa. Hukumar zaben ta ce tana sa ran bayyana illahirin sakamakon zaben a karshen wannan mako. Sai dai tuni madugun 'yan adawar kasar ya yi yi kira da a soke zaben wanda ya ce an tamka dan karen magudi a cikinsa.